
Wasu Bidiyo na yawo a kafafen sada zumunta cewa, wai Motar G-Wagon ta Nazir Ahmad Sarkin Waka ta yi Hadari.
An ga Bidiyon wata G-Wagon inda aka hadata da hotunan Nazir Ahmad Sarkin Waka.
Saidai babu tabbacin gaskiyar lamarin domin Sarkin Wakan da kansa bai bayyana haka ba, kuma babu wani na kusa dashi daya bayyana hakan.
Nazir Sarkin Waka dai ya bayyana cewa, motar tasa ta G-Wagon zata sayi ta Rarara guda 3 har da canji.