
Malamin addinin Islama, Sheikh Lawal Triumph ya bayyana cewa dama babu abinda ya hada dan Izala da yin fim.
Ya bayyana hakane a matsayin martani ga kalaman tauraron fina-finan Hausa, Tijjani Faraga bayan da yace shi ba dan izala bane kuma duk wanda ya kara hadashi da Izala bai yafe ba.
Lawal Triumph yace dama daga Maulidi ake fara harkar fim idan an samu ci gaba shine za’a shiga a ci gaba a kai masana’antar fina-finan Hausa.
Malam yace Tijjani yana tunanin ya zagi Izala ne amma yabonta yayi, yace dan babu dan fim dan izala, babu boka dan izala, babu dan daudu dan Izala.