
Babban Fasto, Elijah Ayodele na cocin INRI Evangelical Spiritual Church ya gargadi shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da cewa ya canja manyan jami’an tsaron dake kusa dashi.
IFasto Elijah Ayodele ya bayyana cewa, idan shugaba Tinubu ya zarce a karo na biyu a mulkinsa, wasu ‘yan Adawa zasu baiwa manyan sojoji makudan kudade su tsigeshi daga mulki.
Faston yace Wahayi aka masa game da wannan lamari.
Ya bayyana shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a matsayin shugaban da ba’a taba yin irinsa ba, inda yace ko Tafawa Balewa da Obafemi Awolowo basu kaishi ba.