Da Ɗumi-Ɗumi: Ɗan Majalissa Mai Wakiltar Argungu A Jihar Kebbi Ya Sauya Sheƙa Daga Jam’iyyar APC Zuwa ADC.

Ɗan majalissar dokoki mai wakiltar ƙaramar hukumar Argungu a zauren majalissar dokokin Jihar Kebbi, Onarabul Nasiru Muhammad Ɗan’umma, (Katukan Kebbi), ya fice daga jam’iyyar APC ya koma sabuwar tafiya ta jam’iyyar haɗaka (ADC).
Bayanin hakan na ƙunshe ne ta cikin wata takardar bayyana ficewa da ɗan majalissar ya aike ga shugaban jam’iyyar APC na mazaɓarsa ta Kakani ta Kudu da ke ƙaramar hukumar Argungu, a birnin Kebbi, kamar yadda Dokin Ƙarfe TV ta ruwaito.

“Ni Onarabul Nasiru Muhammad Ɗan’umma, na jam’iyyar APC, daga yau 7 ga watan Yuli, 2025 na fita daga jam’iyyar APC na koma sabuwar tafiya ta jam’iyyar ADC. Ina fatan Allah Ya Yi mana abin da ya fi zama alkhairi gare mu gaba ɗaya, Na gode”. Cewar Ɗan majalissar.