Ana Zargin Magoya Bayan Sarki Aminu Ado Bayero Da Kai Hari Fadar Sarki Sanusi II

A jiya Lahadi, an sami rikici a birnin Kano bayan da magoya bayan tsohon sarkin Kano, Aminu Ado Bayero, suka kai hari fadar Sarkin Kano mai ci, Muhammadu Sanusi II, dake Kofar Kudu.
Rahotanni sun nuna cewa magoya bayan Bayero sun kutsa cikin fadar, inda suka raunata wasu daga cikin masu gadi tare da lalata wasu motocin ‘yan sanda da na fadar. Shaidu sun bayyana cewa harin ya faru ne lokacin da Sarkin ya dawo daga tafiya tare da rakiyar sa.
Mai magana da yawun fadar, Sadam Yakasai, ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya ce an karya ƙofar shiga fadar, an raunata masu tsaro sannan an lalata wasu motocin jami’an tsaro.
Sai dai wani daga cikin tawagar Bayero, Muktar Dahiru, ya musanta zargin kai hari. A cewarsa, wasu bata-gari ne suka tare su a hanya, kuma sai suka nemi kare kansu. Ya kara da cewa ‘yan sanda ne suka yi amfani da hayaki mai sa hawaye domin shawo kan rikicin.
Har yanzu rundunar ‘yan sanda a jihar Kano ba ta fitar da sanarwa ba dangane da faruwar lamarin, kuma ba a tabbatar da kama kowa ba.
Wannan rikicin na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun rashin jituwa a tsakanin magoya bayan Sanusi da Bayero, tun bayan da gwamnatin jihar Kano ta dawo da Muhammadu Sanusi II matsayin sarki a watan Mayu.
Jama’a na kira da a dauki matakan da suka dace domin kauce wa sake afkuwar irin wannan rikici a gaba.