
Rahotanni na yawo cewa, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party, Peter Obi na iya ficewa daga hadakar jam’iyyar ‘yan Adawa ta ADC.
Me gabatar da shirye-shirye na Arise TV, Rufa’i Oseni ne ya bayyana hakan inda yace idan hakan ta tabbata, kuri’ar ‘yan adawa zata rabu wanda hakan zai iya baiwa Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu damar sake cin zabe.
Rahotanni sun ce, Manyan ‘yan Adawar na ADC, Atiku Abubakar, Peter Obi, da Rotimi Amaechi duka suna son samuj tikitin tsayawa takarar shugaban kasa a jam’iyyar.
Wannan ne ake ganin dama zai jawowa hadakar ‘yan adawar matsalar rarrabuwar kai.