
Rahotanni daga Abuja na cewa, mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya caccaki shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu kan dakatar da gwamnan jihar Rivers, Simi Fubara.
Kashim yayi wannan naganane a wajan kaddamar da wani littafi da ya halarta.
Ya ce a lokacin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan yana mulki, ya so ya cireshi a matsayin gwamna dalilin matsalar tsaro.
Saidai kakakin majalisa a wancan lokacin Aminu Waziri, Tambuwal bai amince ba.
Hakanan babban lauyan gwamnatin Goodluck Jonathan, Bello Adoke ma ya gayawa Jonathan din cewa bashi da hurumin cire Gwamnan.
Yace Hakanan Jonathan ya tambayi Lauya Kabiru Turaki SAN kan maganar amma yace masa hakan ya sabawa doka.
Shettima dai bai yi magana kai tsaye game da cire Fubara da Tinubu yayi ba.
An yi kokarin jin ta bakin fadar shugaban kasa kan lamarin amma abin ya ci tura.