
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya dawo daga Kasar Brazil inda ya halarci taron kungiyar kasashen BRICS.
Manyan jami’an Gwamnati ne suka karbeshi a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe dake Abuja.

Me magana da yawun shugaban kasar, Bayo Onanuga ya tabbatar da dawowar shugaban kasar.

Yace daga cikin wadanda suka karbi shugaban kasar a filin jirgi akwai ministan kasafin kudi, Atiku Bagudu, Karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle, babban me baiwa shugaban kasa shawara kan harkar tsaro, Nuhu Ribadu, jigo a jam’iyyar APC, Ibrahim Masari, da tsohon gwamna jihar Sokoto, Aliyu Wamakko.
Kamin kasar Brazil, shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya fara ziyartar kasr Saint Lucia ne.