
Rahotanni daga jihar Katsina na cewa, tawagar da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya tura dan kula da jana’izar tsohon shugaban kasa, marigayi, Muhammadu Buhari ta isa Katsina.
Ana tsammanin da misalin karfe 2 na ranar yau ne za’a yi jana’izar tsohon shugaban kasar a mahaifarsa dake Daura.
Tuni manyan mutane suka cika daura dan halartar jana’izar.