Monday, December 16
Shadow

Kaduna: Kotu Ta Dawo Da Wani Babban Basarake da El-Rufa’i Ya Tsige

Kotun masana’antu ta kasa da ke zamanta a Kaduna a ranar Litinin din da ta gabata ta yi watsi da tsige babban sarkin Piriga da ke karamar hukumar Lere, Cif Jonathan Pharaguwa Zamuna.

Da yake yanke hukuncin, Mai shari’a Bashir Attahiru Alkali, bayan ya tabbatar da cewa kotun masana’antu ce ke da hurumin sauraron shari’ar, ya ce gwamnatin tsohon Gwamna El-Rufai ba ta bi ka’ida ba wajen tsige sarkin Piriga mai daraja ta uku tare da ayyana aikin ya sabawa kundin tsarin mulki, ba bisa ka’ida ba, rashin adalci, maras amfani, kuma ba shi da wani tasiri.

Kotun ta bayar da umarnin mayar da Cif Zamuna kan karagar mulki tare da biyan duk wani albashi da kuma alfarmar da aka ba shi.

Karanta Wannan  Hotunan mata 2 da suka fito takarar shugaban kasa a kasar Iran

Sannan ta umarci gwamnatin jihar Kaduna da ta biya Cif Zamuna diyyar Naira miliyan 10 saboda tauye masa hakkinsa da aka yi, tare da bayar da umarnin yin aiki da hukuncin a cikin kwanaki 30.

Da take mayar da martani kan hukuncin, Henrietta Iorkumbul Esquire, wacce ta wakilci babban lauyan mai da’awar, Napoleon O. Idenala Esquire, ta bayyana sauraron adalci a matsayin mabudin adalci da bin doka.

James Kanyip Esquire, wanda ya wakilci babban lauya ga wanda ake kara da kuma gwamnatin jihar Kaduna, ya ki cewa komai game da hukuncin.

Da yake zantawa da manema labarai, babban hakimin Piriga da aka dawo da shi, Cif Zamuna, ya cika da godiya bisa yadda aka yi adalci da gaskiya.

Karanta Wannan  Kalli Hotuna: Ga Mahajjata A Filin Jirgi, Ga Kuma Ma'aikatan Filin Jirgi Sun Fantsama Yajin Aiki!

A ranar 22 ga watan Mayun shekarar 2023, tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai, ya sanar da tsige wasu manyan sarakuna guda biyu, sarkin Piriga da na masarautar Arak da ke unguwar Sanga, inda ya bayyana cewa, “bayan bayanan sun biyo bayan shawarwari daga ma’aikatar kula da harkokin kananan hukumomi daidai da tanadin sashe na 11 na dokar cibiyoyin gargajiya mai lamba 21 ta shekarar 2021,” a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kwamishiniyar al’amuran kananan hukumomi, Hajiya Umma Ahmad.

Sai dai Cif Zamuna ya garzaya kotun masana’antu inda ya bukaci ta ajiye wannan kujera saboda rashin samun adalci, domin ba a yi masa wata tambaya ba ko kuma aka gayyace shi ya bayyana nasa labarin kan zargin da ake masa.

Karanta Wannan  Akwai barazanar ambaliya a jihohi 31 da ƙananan hukumomi 148'

Daga: Abbas Yakubu Yaura

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *