
Gawar tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ta isa Daura inda za’a yi jana’izar sa da yammacin yau.
Gawar ta samu rakiyar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima da sauran manyan mukarraban gwamnati.
Nan gaba kadan za’a binne Buharin.