
Jikar tsohon shugaban kasa, Marigayi, Muhammadu Buhari me suna Sa’adatu Muhammad ta bayyana irin rasuwar da kakanta yayi.
Sa’adatu tace ya rasu yana kalmar shahada kuma ko shakuwa bai yi ba.
Ta bayyana hakane a hirar da BBChausa suka yi da ita inda tace yayi cikawa me kyau.
Tace game da yanda ya gudanar da mulki, a kullun Talaka ne a bakinsa, ya ki yadda a cire tallafin man fetur sannan ya bayar da tallafi ga manoma.