
Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya rasu a Asibitin London Clinic wanda da yawa da jin sunan sun dauka karamin Asibiti ne kamar yanda ake cewa Clinic a Najeriya.
London Clinic na daya daga cikin manyan Asibitoci masu zaman kansu a kasar Ingila wanda ke duba manya mutane da suka hada da ‘yan siyasa daga kasashe daban-daban na Duniya.
Hatta Iyalin Masarautar Ingila na zuwa wanna Asibiti.
Ana biyan kudade masu tsada waja kwanciya a wannan Asibiti wanda shiyasa da yawa ‘yan kasar basa iya zuwansa sai masu inshorar Lafiya me tsada sosai.
Wasu likitocin Najeriya dake aiki a kasar Ingila da jaridar Punchng ta zanta dasu sun bayyana irin kudaden da ake biya wajan kwanciya a wanan asibiti.
Daya daga ciki yace, Idan mutum zuwa kawai zai yi a dubashi a Asibitin ya koma gida ana karnar Naira Dubu dari da saba’in zuwa Naira Miliyan daya da dubu dari biyar.
Idan kuma kwantar da mutum za’a yi, ana biyan tsakanin Naira Miliyan daya da dubu dari bakwai zuwa Naira Miliyan shidda da dubu dari biyu.
Ba shugaba Buhari ne kadai ya kwanta a Asibitin ba, hadda tsohon shugaban kasa, Abdulsalam Abubakar saidai shi ya warke inda shi kuma shugaba Buhari a rasu.
Kungiyar Likitocin Najeriya ta koka da yanda shuwagabanni basa gyara asibitocin da ake dasu a gida maimakon hakan sun kwammace su je kasashen waje neman lafiya.