Karin Bayani Game Da Haďarin Da Gwamnan Jihar Katsina Ya Yi.

Motar Gwamnan Katsina ce tayi taho mu gamu da wata mota Golf cikin daren nan har saida motar Golf din injinta ya fita sanadiyar mai Golf din yayi lodi mai yawa hade da dan zaman gefen direba hakan yasa ya kasa rike motar tashi, duk kusan mutanen cikin motar sun kakkarye.
A motar Gwamnan kuma su uku ne da Chief of Staff da wani dan majalisar tarayya wanda shi kam ya karye a cinya, Chief of Staff kuma yaji jiki sosai.
Shima mai girma Gwamna ya bugu sosai a kirjinshi an dauke shi daga asibitin Daura zuwa wani wuri na daban.
Hatsarin ba’a Convoy ya faru ba, fita ce suka yi Privately kamar ba tafiyar Gwamna ba.
Daga Abba Sani Pantami