Friday, December 5
Shadow

YANZU-YANZU: An Fara Gudanar Da Zàñga-zàñgar Kan Karin Albashi Da Fanshøɲ ‘Yan Sanda Masu Aiki Da Masu Ritaya

YANZU-YANZU: An Fara Gudanar Da Zàñga-zàñgar Kan Karin Albashi Da Fanshøɲ ‘Yan Sanda Masu Aiki Da Masu Ritaya.

Daga Muhammad Kwairi Waziri

Yayin wata gagarumar zanga-zanga da aka gudanar a yau, Omoyele Sowore, ɗan gwagwarmaya kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, ya jagoranci gungun masu zanga-zanga domin neman a inganta rayuwar jami’an ‘yan sanda a Najeriya.

Masu Zãɲgà-Zàɲģà sun bukaci gwamnati ta duba halin kuncin da ‘yan sanda ke fuskanta, musamman yadda albashinsu ke ƙasa da kima, tare da rashin kula da ‘yan sanda da suka yi ritaya. Sun ce lokaci ya yi da za a mutunta waɗanda ke bayar da rayukansu don kare lafiyar jama’a da dukiyarsu.

Karanta Wannan  Matsalar tsaro ta janyowa Najeriya asarar Naira Tiriliyan 7.17 sannan kaso 40 na dabbobin da ake dasu sun salwanta saboda matsalar

Sowore ya bayyana cewa, “Yan sanda su ne ginshiƙin tsaro a ƙasa, amma ana wulaƙanta su da iyalansu. Ba za mu ci gaba da shiru ba alhali suna rayuwa cikin talauci bayan shekaru da dama na hidima.”

Masu zanga-zangar sun rike kwalaye masu ɗauke da rubuce-rubuce kamar:

“A biyan ‘yan sanda albashi mai kyau yanzu!”

“Rayuwa mai kyau ga masu ritaya!”

“’Yan sanda ma mutane ne!”

Zàñga-zàñgar ta gudana cikin lumana, tare da jami’an tsaro da suka tabbatar da zaman lafiya a wajen.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *