Friday, December 5
Shadow

ADC ce ke amfani da rasuwar Buhari don neman karɓuwa ba ji ba>>Shugaba Tinubu

Fadar Shugaban Najeriya ta mayar da martani kan zargin da jam’iyyar haɗaka ta ADC ta yi na cewa gwamnatin shugaba Bola Tinubu na amfani da rasuwar tsohon shugaba Muhammadu Buhari, don samun tagomashi na siyasa da neman karɓuwa a idon jama’a.

Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai, Sunday Dare ya bayyana zargin na ADC a matsayin “abin kunya,” inda ya ce jam’iyyar ce ke amfani da rasuwar Buhari don neman suna.

ADC dai ta ce gwamnatin Tinubu ta yi amfani da yadda aka gudanar da jana’izar Buhari da kuma yadda aka shirya bikin bankwana da shi a Daura da ke jihar Katsina, domin ƙara samun ƙarbuwa a idon ƴan ƙasa.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon: Inda wata matar aure ke bada labarin cewa abokin aikinda a ofis da suke aikata alfasha tare yafi mijinta iya sarrafa mace

Fadar shugaban ƙasar ta ce marigayi Muhammadu Buhari ya cancanci yi masa jana’izar ban-girma kuma sun yi haka ne don girmamawa saboda hakan ne ya dace da shi a matsayinsa na tsohon shugaban ƙasa.

Ɓangarori da dama a Najeriya sun yaba da karramawar da gwamnatin ta Tinubu ta yi wa marigayin, sai dai masu suka sun ce gwamnatin na yi ne domin “lallaɓa masoya tsohon shugaban ƙasar da nufin janyo su a jika”.

Ana kallon Buhari a matsayin ɗaya daga cikin ƴan siyasa mafiya karɓuwa tsakanin al’umma a tarihin Najeriya.

ADC, jam’iyya ce wadda ƴan siyasa masu adawa da gwamnatin ƙasar suka tare a cikinta da nufin haɗa ƙarfi wajen yaƙar jam’iyyar APC mai mulki a babban zaɓen ƙasar da za a yi a 2025.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon: Allah ya yadda da Lamarin mu, Wallahi daren jiya na yi mafarki da Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam)>>Inji Malam

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *