
Babbar Kotun tarayya dake Maitama Abuja ta hana tsohon gwamnan jihar Kogi Yahya Bello Fasfo dinsa dan ya je kasar waje neman magani.
Mai shari’a Justice Emeka Nwite ya bayyana wannan hukunci.
Yace takardun da Tsohon gwamnan ya gabatar na neman ya tafi kasar ingila basu da tambarin sarki wanda kotun tace basu da wani amfani a wajanta.
Dan haka tace kuma rashin lafiyar ta tsohon gwamnan ba ta yi tsananin da za’a ce sai an fitar dashi kasar waje ba.
Ana zargin tsohon gwamnan da dan uwansa, Ali Bello, Dauda Suleiman da Abdulsalam Hudu wajan satar Naira N80, 246,470, 088.88.