Friday, December 5
Shadow

Kalli Bidiyo: Ko dai auren Sadiya Haruna ba da gaske bane? Wanda ake cewa shine sabon Mijinta(Kilishi) ya fito yace ba gaskiya bane

{“remix_data”:[],”remix_entry_point”:”challenges”,”source_tags”:[“local”],”origin”:”unknown”,”total_draw_time”:0,”total_draw_actions”:0,”layers_used”:0,”brushes_used”:0,”photos_added”:0,”total_editor_actions”:{},”tools_used”:{},”is_sticker”:false,”edited_since_last_sticker_save”:false,”containsFTESticker”:false}

A wani lamari na ba zata, mutumin da ya karade kafafen sada zumunta wanda aka yi ta watsa cewa, shine sabon mijin Tauraruwar Tiktok, Sadiya Haruna, ya fito yace ba shi bane.

Sadiya Haruna dai ta bayyana yin sabin aure bayan rabuwa da tsohon mijinta wanda take kira da Best Choice.

Saidai bata bayyana sabon mijin nata ba wanda saidai ta rika nuna Bidiyon su tare amma ba fuska.

Da yawa musamma mata sun rika fadin cewa, Sadiya Haruna na da farin jini ganin cewa da aurenta ya mutu sai ta samu ta kara yin wani auren.

Saidai Wanda ake cewa shine sabon mijin nata ya fito yace basi bane kuma bashi da alaka da ita amma yana mata fatan Samun miji na gari.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Anata cece-kuce bayan da Tauraruwar Kannywood A'isha Najamu ta bayyana kanta a matsayin 'yar Shi'a

Hakan yasa wasu suka rika tunanin ko dai dama auren nata ba gaskiya bane?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *