
Tsohon Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom ya bayyana cewa, ba zai shiga hadakar jam’iyyar adawa ta ADC ba.
Yace ba zasu yi nasara ba, Tinubu ne zai sake cin zabe.
Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a gidan talabijin na Channels TV ranar Litinin.
Yace suran na da ‘yancin shiga jam’iyyar ta ADC amma shi ka yana nan a jam’iyyar PDP ba zai fita ba.
Ortom yace ko da ADC ta yi nasarar magance matsalolin da take fama dasu ba zata iya cin zabe ba.