Friday, December 5
Shadow

Duk da matsin rayuwa, Hukumar NBS tace Tattalin arziƙin Najeriya ya ƙaru da kashi 3.13 a farkon 2025

Tattalin arzikin Najeriya ya ƙaru da kashi 3.13 cikin 100 a watanni uku na farkon shekarar 2025, a cewar rahoton Hukumar Kididdiga ta Ƙasa (NBS).

Sanarwar da NBS ɗin ya fitar ranar Litinin, ta ce wannan ya zarta kashi 2.27 cikin 100 da aka samu a irin wannan lokaci a shekarar 2024.

Rahoton ya ce ɓangarorin da suka fi ba da gudummawa wajen haɓakar tattalin arziƙin sun haɗa da na ayyuka da kuma masana’antu.

A lokaci guda kuma an sabunta ƙididdigar GDP daga shekarar 2019, inda sabon adadin ya kai naira tiriliyan 205, a cewar shugaban hukumar ƙididdiga ta ƙasa, Adeyemi Adeniran.

Ya bayyana cewa sabon adadin ya ƙaru da kashi 41.7 cikin 100 idan aka kwatanta da na shekarar 2014.

Karanta Wannan  An shawarci Atiku cewa kar ya hada kai da El Rufai, domin zai sake yin kuskuren da yayai abaya ne, lokacin daya kai El Rufai wurin Obasanjo amma ya juya masa baya

Adeniran ya ƙara da cewa sassa guda biyar da suka fi taka rawa wajen wannan ci gaban sun haɗa da: noman da kasuwanci da ɓangaren masana’antu da kamfononin sadarwa da kuma man fetur da iskar gas.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *