Friday, December 5
Shadow

Kananan yara 3 sun rigamu gidan gaskiya yayin da suke wanka a rafi a jihar Bauchi

Rahotanni daga jihar Bauchi na cewa wasu yara 3 dake wanka a wani rafi dake kauyen Jinkiri na karamar hukumar Bauchi a jihar Bauchi sun rigamu gidan gaskiya.

Kakakin ‘yansandan jihar, Ahmad Wakili ya tabbatar da faruwar hakan ga manema labarai ranar Laraba a Bauchi.

Ya bayyana sunaye da shekarun yaran da suka rasu kamar haka: Habibu Mohammed, 16, Abubakar Mohammed, 16, da Zailani Sule, 14, yace dukansu sun fito ne daga kauyen Durum.

Kuma sun rasu ranar Lahadi da misalin karfe 1 na rana.

Yace yaran na aikin hakar ma’adanai ne kamin zuwa su yi wanka, yace an yi kokarin kaisu asibiti amma akan hanya suka rasu kamin a karasa.

Karanta Wannan  Wike ya bayar da umarnin a kulle sakatariyar jam'iyyar PDP dake Abuja

Yace likitoci sun tabbatar da mutuwar yaran kuma ana shirin mikasu wajan danginsu dan su binnesu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *