
Kamfanin dake kula da wutar lantarki na kasa,NERC yace jihar Enugu dake son rage farashin wutar lantarki da mutanen jihar ke biya bata da hurumin yin hakan.
Jihar Enugu dai ta bayyana shirinta na rage farashin wutar lantarki da mutanen dake tsarin Band A ke biya Wanda jihar tace yayi yawa.
Saidai hukumar NERC tace jihar dama duk wata jiha dake tunanin yin hakan bata da hurumin yin hakan.
NERC tace duk jihar dake son yin hakan, saidai ta rika biyan tallafi ko kuma idan ba zasu iya biyan tallafin ba, to dole mutane su rika biyan cikakken kudin wutar lantarkin.
Hakan na zuwane yayin da suma kamfanonin dake rarraba wutar Lantarkin, DISCos ke cewa jihohin su jira sai sun fara samarwa da rarraba wutar lantarkinsu kamin su fara cewa zasu kayyade farashin wutar.