
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa taron rudaddu ne suka kafa jam’iyyar ADC.
Shugaban ya bayyana hakane a wajan babban taron jam’iyyar APC wanda aka yi jiya inda anan aka zabi Prof. Nentawe Yilwatda a matsayin sabon shugaban jam’iyyar.
Shugaba Tinubu yace sauran ‘yan siyasar dake jam’iyyun Adawa su bar jirgin ruwa me nutsewa su dawo jam’iyyar APC.