Friday, December 5
Shadow

Dan kudu zamu tsaida takarar shugaban kasa a 2027>>Inji Jam’iyyar PDP

Jam’iyyar PDP ta sanar da cewa, dan kudu zata tsayar takarar shugaban kasa a shekarar 2027.

Jam’iyyar ta bayyana hakane a zaman masu ruwa da tsaki da ya wakana a jiya.

Sannan ta canja wajan da zata gudanar da taronta na zaben shuwagabannin jam’iyyar wanda a da za’a yi a Kano, yanzu a jihar Oyo za’a yi.

Ana zargin an yi hakanne dan shiryawa gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinda hanya a shirinsa na tsayawa takarar shugaban kasa a 2027.

Saidai hakan kuma zai zama koma baya ga Nyesom Wike wanda tuni dangantaka tsakaninsa da Gwamna Makinde ta yi tsami.

Karanta Wannan  Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zai kai ziyara jihar Kaduna, Gobe Juma'a

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *