Friday, December 5
Shadow

Ga ‘Yan Najeriya na fama da yunwa, ga rikici tsakaninka da Kashim Shettima amma jam’iyyar mu ta ADC ce ta tsone maka ido>>Atiku ga Shugaba Tinubu

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya mayarwa da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu martani kan sukar da shugaban kasar yayi ga jam’iyyar ADC.

Shugaba Tinubu a wajan taron jam’iyyar APC inda aka zabi sabon shugaban jam’iyyar ya bayyana cewa mutanen jam’iyyar ADC rikitattun mutanene.

Saidai a martaninsa, Atiku yace akwai abubuwa da yawa da ya kamata Shugaba Tinubu ya mayar da hankali kansu maimakon sukar jam’iyyar ADC wanda ya mayar abin yi kullun.

Yace tattalin arzikin Najeriya na cikin halin ni ‘yasu, ‘yan Najeriya na cikin yunwa, sannan ga rikici tsakaninshi da mataimakinsa, Kashim Shettima wadannan abubuwan ya kamata ya mayar da hankali kansu ba sukar jam’iyyar ADC ba.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Wata Sabuwar Masifa ta Shigo kafafen sada zumuntar Arewa inda ake cin zarafin malamai ta hanyar Amfani da AI asa su yi rawa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *