Friday, December 5
Shadow

Bamu Yadda ba: Kungiyar Malaman Jami’a ta Najeriya, ASUU za ta kai karar shugaba Tinubu Kotu saboda sakawa jami’ar UNIMAID dake Maiduguri sunan Muhammad Buhari

Kungiyar malaman Jami’a ta ASUU tace zata kai karar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu kotu saboda sakawa jami’ar UNIMAID dake Maiduguri sunan tsohon shugaban kasa, Marigayi Muhammadu Buhari.

Kungiyar tace ta cimma wannan matsaya ne bayan taron data gudanar wanda ya hada hadda wakilan kungiyar dalibai.

Sanarwar bayan taron da aka fitar ranar Juma’a wadda ta samu amincewar shugaban kungiyar Abubakar Mshelia da mataimakin sakatare na kungiyar, Peter Teri tace basu amince da wannan mataki ba.

Hakanan sanarwar tace an dauki wannan mataki ne ba tare da tuntubar ma’aikatan jami’ar da kungiyar ta ASUU ba da kuma kungiyar daliban da suka kammala makarantar a baya ba.

Karanta Wannan  Bincike: An bayyana jihohin da maza suka fi neman mata dan aikata Alfasha a Najeriya

Sanarwar tace canja sunan zai shafin tarihin da makarantar ta kafa na tsawon shekaru 50 da suka gabata.

Dan haka ace bata amince ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *