
Rahotanni sun tabbatar da cewa, zuwa na karshe da Tsohon Gwamnan Kano, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso yayi zuwa fadar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu bai samu ganin shugaban kasar ba.
An ruwaito cewa Kwankwaso da shugaba Tinubu sun gana ranar Litinin din data gabata.
Saidai Rahoton Daily Trust yace ba’a yi ganawa tsakanin Tinubu da Kwankwaso ba.
Daily Trust tace wani taro ne ya kai Kwankwaso fadar shugaban kasar amma ba ganawa da Tinubu ba.
Daily Trust ta kara da cewa majiyoyi na kusa da shugaban kasar sun tabbatar mata da cewa babu wata ganawa da aka yi tsakanin shugaba Tinubu da Kwankwaso.