Monday, December 16
Shadow

Gwajin ciki na sati daya

Bayan yin jima’i ba tare da kariya ba ta kwaroron roba, watau Kondom, mace zata iya daukar ciki.

Kuma zaki so yin gwaji da ganin kin dauki cikin ko baki dauka ba?

Saidai masana sun bayyana cewa, sati daya yayi kadan ki gane cewa kin dauki ciki ko baki dauka ba.

Mafi abinda ya dace a yi shine a dakata har sai bayan kwanaki 10 zuwa sati 2 da yin jima’i kamin a fara yin gwajin ciki.

Wasu kuma sun bayar da shawarar a jira sai bayan daukewar jinin al’ada. Ana iya yin gwajin ciki ranar farko da aka yi batan wata.

Jira zuwa lokaci me tsawo watau sati 3 zuwa 4 bayan an yi jima’i ba tare da kariyar kwaroron roba ba, watau kondon kamin a yi gwajin ciki, ya fi bayar da sakamako me kyau.

Karanta Wannan  Yadda ake gwajin ciki da allura

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *