Friday, December 5
Shadow

Mu ‘yan Arewa bamu yi dana sanin Zaben Tinubu ba>>Inji Ministan tsare-tsare, Atiku Bagudu

Ministan tsare-tsare Atiku Bagudu ya bayyana cewa, ‘yan Arewa basu yi dana sanin zaben shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ba.

Ya bayyana hakane a wajan taron Arewa House da aka yi na kwanaki biyu tsakanin shuwagabanni da wanda akw Mulka a jihar Kaduna.

Ministan yace a lokacin kamin Tinubu ya hau mulki ana ta ciwo bashi ana siyo man fetur daga kasashen waje sannan ana biyan kudin tallafi.

Yace amma da Tinubu yazo ya dakatar da duka wannan sannan ya cire tallafin man fetur dana dala.

Yace bayan cire tallafin man fetur jihohi sun samu karin kudaden shiga.

Dan haka yayi kira ga mutanen Arewa da su daina sauraren masu kokarin hure musu kunne kan cewa wai shugaba Tinubu ya ware Arewa baya mata komai a gwamnatinsa.

Karanta Wannan  Trump ya naɗa Elon Musk shugaban ma'aikatar inganta aikin gwamnati

Yace Gwamnatin Tinubu na tafiya tare da ‘yan kasa wajan gudanar da mulki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *