
Kungiyoyin ‘yan kasuwar Man fetur, NOGASA, PETROAN sun bayyana rashin jin dadinsu da yunkurin Aliko Dangote na fara kai man fetur din zuwa gidajen mai da motocinsa na jigilar da ya siyo.
‘yan kasuwar sun ce Dangote ba zai iya yin wannan aiki shi kadai ba.
Sun ce idan kuwa yace zai yi, to zai kawo rudani ne a kasuwar man fetur din.
Kungiyoyin sun koka da cewa, Dangote ya dauki wannan mataki ne ba tare da tuntubar masu ruwa da tsaki a harkar ba.
Sun yi kira ga shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da ya shiga maganat.
Shugaban NOSAGA, Bennett Korie ne ya bayyana hakan a Abuja ranar Alhamis a wajan babban taron kungiyar.
Shima Shugaban PETROAN, Billy Gillis-Harry ya jadada hakan.
Saidai a martanin matatar Dangote, tace ‘yan kasuwar suna wannan babatu ne kawai dan basu son ci gaban Najeriya.