Friday, December 5
Shadow

Bidiyo: Na tafka Kuskure sosai a rayuwata, ko makiyi na ban so ya shiga wahalar dana shiga, Akwai sanda ake ta so a aureni, naki amma yanzu kuma so nake in yi aure kamin in koma ga mahalicci na>>Inji Ummi Nuhu a sabuwar hirarta

Tsohuwar Tauraruwar fina-finan Hausa, Ummi Nuhu ta bayyana cewa, akwai sanda ake ta son aurenta amma bata maida hankali ba.

Tace amma yanzu ta na son ta yi aure kamin komawa ga mahaliccinta.

Ummi ta bayyana hakane a sabuwar hirar da BBChausa ta yi da ita inda tace ko makiyinta bata son ya shiga wahala rayuwar data shiga.

Saidai Ummi tace ida kuma Allah ya kaddaro cewa a haka zata mutu ba tare da yin aure ba, zata rungumi kaddararta.

An fara jin halin da Ummi ke ciki nw bayan hirar da Hadiza Gabon ta yi da ita a shirin ta na Gabon Show da ta ke yi a YouTube channel dinta.

Karanta Wannan  Hotuna: Rahama Sadau da Rahama Saidu an Hadu

Da yawa dai sun tausayawa Ummi Nuhu inda aka rika tara mata kudi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *