
Rahotanni na cewa, Mummunan Hadarin mota ya rutsa da Tauraruwar Kannywood, Samha M. Inuwa.
Hakan ya farune yayin da take kan hanyarta ta komawa Kano daga wajan bikin data halarta a Kaduna.
Motar su Samha ta daki Trela ne ta baya wanda yasa ta lalace.
Gfresh Al-amin ya bayyana cewa sun yi waya kuma ta sanar dashi tana bukatar addu’a.
Shima Hassan Make-Up ya wallafa hotunan Samha yana kuka da kiran a sakata a addu’a.