Tuesday, May 19
Shadow

Idan Tinubu ya sake cin zabe, Najeriya ba zata kai Labari ba, Inji Malam Nasiru Ahmad El-Rufai

TIRƘASHI: Zai yi Wuya Nijeriya ta Ci Gaba da Rayuwa Idan Tinubu ya Zarce a 2027 – El-Eufai

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, kuma Korarren Ministan da majalisa ta ƙi tantance wa, Malam Nasir El-Rufai , ya bayyana cewa makomar Najeriya na cikin hadari idan jam’iyyar APC ta ci gaba da mulki bayan 2027.

Jaridar Sahara Reporters ta rawaito cewa El-Rufai ya bayyana hakan ne a Sakkwato yayin wani gangamin wayar da kan jama’a na jam’iyyar hamayya ta hadaka, African Democratic Congress (ADC), inda ya ce yana cikin siyasa ne don ceto kasa, ba don wata riba ba.

Ya ce ya fice daga APC ne saboda gazawarta wajen tafiyar da mulki, yana mai gargadin cewa ci gaban mulkin APC zai iya rusa tubalin zamantakewa na kasar.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon: Yanda aka baiwa Mawakin Kudu, Asake damar yin Sallah a guri na musamman da ba kowa ake baiwa damar shiga ba a Harami yayin da yaje Umrah

El-Rufai, wanda yanzu ke daya daga cikin jiga-jigan ADC, ya sha alwashin hada kai da ’yan Najeriya domin kifar da gwamnatin APC a matakin jihohi da tarayya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *