
Sanata Abdulaziz Musa ‘Yar’adua ya bayyana cewa, ba gaskiya bane rade-radin da ake yadawa cewa wai ya bar jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar ADC.
Yace har yanzu yana nan a tare da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da gwamnan Katsina, Dikko Radda da kuma jam’iyyar APC.
Yace ba duka masu amfani da sunan ‘Yar’adua ne ke da alakar siyasa iri daya da tashi ba.
Ya zargi wasu kafafen yada labarai da neman yada jita-jita game da komawarsa ADC.
Yace amma shi Har yanzu dan APC ne kuma zai ci gaba da aikin da shuwagabanni dan kawo ci gaba da hadin kan Najeriya.