Friday, December 5
Shadow

Gwamnatin Kano za ta mayar da gidan yarin Kurmawa gidan tarihi

Gwamnatin jihar Kano ta ɓullo da shirin mayar da gidan yarin Kurmawa – da ya kwashe shekara fiye da 100 – gidan tarihi domin adana abubuwan da suka faru lokacin mulkin mallaka.

Gidan yarin mai shekara 115, an gina shi ne lokacin Turawan mulkin mallaka a kusa da fadar sarkin Kano domin a riƙa ɗaure masu laifi a ciki.

A bisa ƙa’idar da aka gina gidan yarin Kurmawa zai ɗauki fursunoni 690 ne kawai

Mai bai wa gwamnan jihar Kano shawara kan harkokin yaɗa labara, Ibrahim Adam ne ya bayyana haka a shafinsa na Facebook.

Ibrahim Adam ya ce za a mayar da fursunonin da ke ɗaure a gidan yarin zuwa sabon gidan fursunan Janguza na zamani, da ke kusa da barikin soji a kan babban titin Kano zuwa Gwarzo.

Karanta Wannan  Kalli Kwalliyar da Rahama Sadau ta yi zuwa wajan Bikin Rarara

Mashawarcin gwamnan Kano ya ce za a mayar da Kurmawa gidan tarihi ne domin taskance abubuwan tarihin da suka faru a zamanin mulkin mallaka.

Sabon gidan yarin Janguza da aka gina a lokacin mulkin tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari zai iya ɗaukar fusrsunoni kimanin 3,000.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *