
Gwamnan Kano Ya Buƙaci Mutumin Dake Shirin Tattaki Zuwa Wajensa Daga Jigawa Ya Koma Gida
Gwamnan Kano ya yi kira ga wani masoyinsa da ke shirin tattaki zuwa wajensa a ƙafa daga Jigawa, Lawan Habib da ya yi zamansa a cikin iyalinsa ba sai ya zo ba.
Gwamnan ta bakin mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya ce addu’ar masoyin nasa yake buƙata ba jefa rayuwarsa cikin haɗari ba.