Monday, August 24
Shadow

Kai Duniya: Ji yanda aka kama ‘ya’ya mata 2 ‘yan uwan juna da suka shirya yiwa mahaifinsu Damfarar Naira Miliyan 5 A Abuja

Hukumar ‘yansandan babban birnin tarayya, Abuja ta kama wasu mata 2 ‘yan uwan juna bisa shirya garkuwa da daya daga cikinsu dan su damfari mahaifinsu Naira Miliyan 5.

Mahaifin nasu me suna Mr. Innocent ne da kansa ya kai karar bacewar diyarsa, Miss Leadway Innocent ‘yar Kimanin shekaru 16 wadda yace tun da ta tafi rubuta jarabawa a Government Secondary School, Karu bata koma gida ba.

Ya kai karar ne ranar 30 ga watan Yuli 2025 inda yace tun ranar 18 ga watan na Yuli diyar tasa ta bace.

Kakakin ‘Yansandan Abuja, SP Josephine Adeh ta tabbatar da faruwar lamarin inda tace mahaifin ya kai korafinne a ofishin ‘yansanda dake Jikwoyi Division.

Karanta Wannan  Gwamnatin Amurka zata fara bukatar 'yan Najeriya dake son zuwa kasar su ajiye dala $15,000(Naira Miliyan Asihirin da biyu) idan mutum ya dawo gida za'a mayar masa da kudinsa, idan kuma ya ki dawowa za'a rike kudin

Yace daga baya an kirashi inda aka ce an yi garkuwa da diyar tasa ne ana neman ya biya kudin fansa.

Tace hukumar ‘yansanda ta bazama bincike inda ta gano diyar mutumin a tare da wasu miji da mata suna sha’aninsu babu wata alamar cewa, an yi garkuwa da itane.

Ci gaba da Bincike yasa an kamo yayar wadda aka sace din me suna Miss Joy Innocent da Saurayinta me suna Mr. Mayowa Adedeji.

Da bincike yayi tsanani an gano Joy Innocent ce ta shirya yin garkuwar karya da kanwarta, LeadWay bisa hadin bakin saurayinta Mayowa Adedeji dan su karbi kudi a hannun mahaifinsu.

Karanta Wannan  Soja Boy ya cewa wanda suka wallafa Bidiyon Kirkira da ya nunashi yana shafa Khirjin Rahama Sa'idu su ji Tsoron Allah

Sannan ita kanta LeadWay ta san da wannan shiri har ma tana taimakawa dan ya tabbata.

Duka su hudun suna hannun ‘yansanda kuma sun amsa laifukan da ake zarginsu da aikatawa.

Nan gaba dai za’a gurfanar dasu a gaban kotu dan zartas musu da hukunci.

Kwamishinan ‘yansandan Abuja, CP Ajao Saka Adewale yayi Allah wadai da wannan abu inda yayi kira ga mutane dasu rika kula da halayyar ‘ya’yansu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *