
Shuwagabannin jam’iyyar ADC na jihohi sun hade kai inda suka ce basu yadda da shugabancin David Mark a matsayin shugaban rikon kwarya na jam’iyyar ba.
Hakan na zuwane a wata sanarwa da shugaban kungiyar tasu me suna,Amb. Elias Adokwu ya sakawa hannu tare da sa hannun sakataren watsa labarai na kungiyar, Godwin Alaku.
Sun bayyana cewa hadakar ‘yan Adawa ta su Atiku karfa-Karfa ta musu.
Sun ce kuma hakan ya sabawa dokokin jam’iyyar.