
Mataimakin shugaban kasa, Kashim shetty ya sauka a garin Akure jihar Ondo inda yake ziyarar aiki wajan taron kaddamar da tallafawa kananan masana’antu.
Me magana da yawun Kashim Shettima, Stanley Nkwocha, ya tabbatar da hakan inda yace Gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa dana Ekiti, Biodun Oyebanji da sauran manyan jami’an gwamnati ne suka tarbi Kashim Shettima a filin jirgin.
An shirya taron ne dan tallafawa kananan masana’antu a matsayin ginshikin ci gaban tattalin arzikin Najeriya.