
Rahotanni sun bayyana cewa, Gwamnatin tarayya karkashin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta kashe akalla Naira Biliyan N26.38bn wajan kula da jiragen saman shugaban kasar a cikin watanni 18 da suka gabata.
Hakan na kunshene a cikin rahoton da kungiyar, Govspend ta fitar wadda ke saka ido akan yanda gwamnati ke kashe kudaden Talakawa.
Rahoton yace an kashe wadannan kudadenne a tsakanin July 2023 zuwa December 2024.
Hakanan rahoton yace shima tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya kashe Naira Biliyan N81.80bn wajan kula da jiragen saman sa a tsakanin shakerar 2016 zuwa 2022.