Friday, December 5
Shadow

Ana tsare da Sowore cikin tasku da cin zarafi – Lauyoyinsa

Lauyoyin ffitaccen ɗan gwagwarmayar nan kuma ɗan jarida, Omoyele Sowore da hukumomin ƙasar ke tsare da shi ya yi kiran sakinsa cikin gaggawa.

Lauyoyin sun yi zargin cewa ana tsare da Sowore ƙarƙashin kulawar babban sifeton ƴansandan ƙasar, cikin hali maras kyau na tasku da cin zarafinsa, lamarin da suka ce yana barazana ga kariyarsa.

A ranar Laraba ne dai aka bayar da rahoton tsare Sowore bayan da ya amsa gayyatar jami’an ƴansanda domin amsa wasu tambayoyi.

Ɗaya daga cikin lauyoyin nasa da ya zanta da sashen Pidgin na BBC, Marshal Abubakar ya ce an gayyacci Sowore ne kan zarge-zargen laufukan bata suna da yin ƙaryar takardun ƴansanda.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Na bar Musulunci na koma Kirista>>Inji Shahararren dan Tiktok Peller, Ji Dalilinsa

Ya ce ƴansanda sun nuna musu wasu takardu na ƙorafi da aka rubuta kan Soworen, yana mai zargin ƴansanda da rubuta ɗaya daga ciki ƙorafe-ƙorafen.

Kawo yanzu dai hukumomin ƴansandan ba su ce komai ba game da tsare Soworen ba, kuma ba su mayar da amsar buƙatar da BBC ta gabatar musu na magana kan batun ba.

Ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama ta Amnesty International ta yi Allah wadai da ci gaba da tsare

Cikin wata sanarwa da ta fitar ta kira ga gwamnatin Najeriya ta saki ɗan gwagwarmayar tare da watsi da zarge-zargen da taje yi masa ba tare da wani sharaɗi ba.

Karanta Wannan  Manufar Amurka akan Najeriya ta fara Fitowa Fili: Dan majalisar Amurka dake gaba wajan Zuga Trump akan Najeriya, Riley Moore yace abinda suke so da Shugaba Tinubu a yanzu shine ya Karfafa Alaka da Amurkar Tunda yace ba gaskiya bane maganar cewa ana Mhuzghunawa Kiristoci

Ƙungiyar ta kuma zargin gwamnatin Najeriya da tauye haƙƙin ƴan ƙasar maimaikon sauraron ra’ayinsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *