
Tsaka Mai Wuya: Har yanzu Atiku yaƙi karɓar katin zama ɗan Jam’iyyar ADC kan jin Jonathan zai koma PDP
Tsohon Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar yaƙi ya karɓi katin zama ɗan Jam’iyyar ADC, a yayinda ake ci gaba da jita-jitar cewa tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan zai yi takara a shekarar 2027.
Atiku, wanda a ƴan kwanakin baya ya fita daga jam’iyyar PDP bayan ɗaukar tsawon lokaci ana rigingimu, an tsara zai karɓar katin jam’iyyar ADC.
Atiku dai zai karɓi katin jam’iyyar ADC a garin sa na Jada da ke ƙaramar hukumar Jada ta Adamawa, an tsara cewa zai karɓi katin jam’iyyar a ranar Laraba 6 ga watan Agusta, amma aka ɗage karɓar katin ba tare da wani bayani ba.
Daga Usman Salisu