
Daga Khalid Yusuf Sambo
Kamar yadda a ke ganin a hoton da ke kasa, shahararriyar Jami’ar nan ta Musulunci ta Duniya da ke Birnin Madinar Manzon Allah (S.A.W) ta ayyana Littafin:
ضوابط الجرح والتعديل عند الحافظ الذهبي
Wallafar Prof. Muhd Sani Umar R/lemo (Hafizahullah) a cikin jerangiyar littafan da za ta yi wa daliban da ke gurbin karatun Digiri na uku (Ph.D) Jarrabawa a cikinsa. Shi ne Littafi daya tilo na mutumin yankin kaf Afirka da ya samu wannan tagomaci.
Hakika wannan yana sake nuna karbuwar Littafin da ficensa a Duniyar ilimi. Da ma kuma Littafi ne da ba a shaida kamarsa a bangarensa ba. Littafin shi ne kundinsa na samun shaidar kammala matakin Digiri na biyu a Jami’ar Musulunci ta Madina, wanda a lokacin ya rabauta na samun koluluwar mataki da jinjina mafi girma a fanninsa.
Allahu Akbar! Allahu Akbar! Allahu Akbar! Allah Ya kara wa wannan Babban Malami Lafiya da Albarka Allah Ya jikan mahaifansa Ya saka masa da Alkhairi.
Mai Rubutu:
Musa Muhammad Dankwano.
Sakataren Kwamitin Ilimi Na Dr. Muhd Sani Umar R/lemo.
23-02-2023.