
Ministan Wutar Lantarkin, Adeboye Adelabu na ci gaba da shan caccaka saboda katafaren gidan da ya nuna wanda ya gina.
Ya gina gidanne a Ibadan jihar Oyo inda aka ganshi a Bidiyon yana Alfahari da hakan.
Da yawa dai sun rika tambayar ina ya samu kudin gina gida irin wannan a dan kankanin lokacin da yayi a matsayin minista?