
Farfesa Sheikh Isa Ali Pantami ya jewa Sanata Aminu Waziri Tambuwal jajen kamen da EFCC suka masa.
An ga Malam a gidan Sanatan dake Abuja inda aka ga sauran manyan ‘yan siyasa a gidan.
Sanata Aminu Waziri Tambuwal ya shafe kwana daya a tsare a hannun EFCC kamin daga baya suka sakeshi.
Jam’iyyar ADC ta yi zargin cewa kamun yunkuri ne na dakile karfin ‘yan Adawa.