Friday, December 5
Shadow

Tinubu zai yi tafiya zuwa ƙasashen Japan da Brazil

Tinubu zai yi tafiya zuwa ƙasashen Japan da Brazil.

Shugaba Bola Tinubu zai kai ziyara zuwa ƙasashe biyu, Japan da Brazil a yau Alhamis, 14 ga watan Agusta.

Bayo Onanuga, mashawarcin shugaban ƙasa na musamman kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, ya ce Tinubu zai tsaya a Dubai, Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), kafin ya zarce zuwa Japan.

Ana sa ran shugaban zai halarci taron ƙasa da ƙasa na tara kan ci gaban Afirka (TICAD9) a birnin Yokohama na ƙasar Japan daga ranar 20 zuwa 22 ga watan Agusta.

Onanuga ya ce Tinubu zai kuma gudanar da tarukan tattaunawa tsakanin ƙasashe da kuma ganawa da shugabannin manyan kamfanonin Japan da ke da hannun jari a Najeriya.

Karanta Wannan  Kotu ta kwace Naira Miliyan 246 daga hannun tsohon soja, Major-General U.M. Mohammed (Retd.)

“Bayan kammala taron TICAD9, Shugaba Tinubu zai tafi birnin Brasilia, babban birnin Ƙasar Tarayyar Brazil, domin ziyarar ƙasa ta tsawon kwanaki biyu daga Lahadi, 24 ga watan Agusta, zuwa Litinin, 25 ga watan Agusta,” in ji sanarwar.

“Wannan ya biyo bayan gayyatar da shugaban ƙasar Brazil, Luiz Inácio Lula da Silva, ya yi masa.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *