
Kafin zaɓen cike gurbi da za a gudanar a gobe, rnanar Asabar a majalisun tarayya da na jiha a Jihar Kaduna, jam’iyyar adawa ta African ADC ta zargi jam’iyyar mai mulki ta APC da daukar ’yan daba da kuma karɓar biliyoyin naira daga cikin jihar da wajen ta domin yin magudi.
Zaɓen cike gurbin zai gudana ne a mazaɓar tarayya ta Chikun/Kajuru da mazaɓar tarayya ta Zaria/Kewaye, da kuma mazaɓar majalisar jiha ta Basawa.
Waɗannan zarge-zargen na ADC sun haifar da musayar maganganu tsakaninta da gwamnatin jihar da kuma jam’iyyar APC.
Kwamishinan ƴaɗa Labarai na jihar, Ahmed Maiyaki da ya mayar da martani yana cewa zarge-zargen na ADC “ba su da tushe kuma abin dariya ne.”