
Mutumin mai suna Shehu Fantage, an kama shine a jiya Juma’a a wani otal dake cikin garin Kaduna, a yayin da yake kokarin kasafta kudin domin yin amfani da su wajen siyen kuri’u a zaben cike gurbi na dan majalisar tarayya mai wakiltar Chikun/Kajuru.
Ita na hukumar ‘yan sandan jihar Kaduna ta bakin kakakinta, DSP Mansir Hassan ta tabbatar da kama mutumin da DSS suka yi, inda yake komar su kuma ana kan bincikensa.