
Jam’iyyar NNPP ta Lashe zaben cike gurbi na Bagwai da Shanono da aka gudanar jiya, Asabar a Kano.
Da yake bayyana sakamakon zaben da misalin karfe 12:36am na safe, Professor Hassan Shitu ya bayyana dan takarar NNPP, Dr Ali Kiyawa a matsayin wanda ya lashe zaben da kuri’u 16,198 inda ya kayar da dan takarar APC, Ahmad Kadamu, da ya samu kuri’u 5,347.
‘Yan Jam’iyyar NNPP sun gudanar da zaman dirshan a ofishin INEC inda suka zargi cewa, ana shirin yin murdiyar zabe a sakamakon mazabar Ghari/Tsanyawa.
Kakakin Gwamnatin jihar Kano, Sanusi Tofa yace ba zasu bar kofar INEC din ba sai an fadi sakamakon Ghari/Tsanyawa