Friday, December 5
Shadow

Cin Amana Ne Zaɓar Shugaban Da Bai Cancanta Ba, Cewar Sheikh Dr. Abdulƙadir Adam Isawa

Cin Amana Ne Zaɓar Shugaban Da Bai Cancanta Ba, Cewar Sheikh Dr. Abdulƙadir Adam Isawa.

Malamin ya bayyana haka ne a karatun littafin Sahihul Bukhari da aka yi zama na arba’in da tara kamar yadda aka saba gudanar da karatun a kowane mako a Masallacin Jami’urrahmah da ke unguwar Kundila a titin Maiduguri na Birnin Kano.

Malamin ya nuna damuwa da takaicinsa kan yadda ake ruɗar mutane da kuɗi kalilan wajen zaɓar miyagun shugabannin da ba su cancanta ba. A ba ka kuɗin da za ka cinye a kwana ɗaya ka zaɓi wanda zai yi shekara huɗu yana azabtar da kai, inda Malamin ya ambaci hakan a matsayin cin amana, kuma hakan yana daga cikin alamomin tashin alƙiyama zaɓar shugabannin da ba su cancanta ba, kawai don sun bayar da taliya.

Karanta Wannan  Dansandan Najeriya ya manto Bìndìgàrsà a gidan giya bayan da yayi mankas

Malamin ya yi karatu a babin da ya bayyana yadda wani Balaraben Ƙauye ya tambayi Manzon Allah SAW game da tashin alƙiyama a lokacin da yake bayar da karatu, sai bayan da ya ƙare karatun ya bayar da amsa, shi ne ya ce idan aka tozarta amana to a jira tashin alƙiyma:

“فإذا ضيعت الأمانة فانتظر الساعه.”

Sai Balaraben Ƙauye ya sake tambaya mene tozartar da amana. Sai Annabi ya ce idan aka ɗora al’amura a inda ba su cancanta ba:

“إذا وسد الأمر إلى غير أهله”

“Idan aka bar wanda ya cancanta aka ɗauki wanda bai cancanta ba don kuɗi ko sanayya ko wani abin daban, wannan duka cin amana.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon yanda Buhari ya koma gidansa na Kaduna da zama bayan kwashe kusan shekaru 2 a Daura

Alamomin tashin alƙiyama sun yawaita, daga cikinsu akwai ƙarancin kunya wanda a halin yanzu muke gani na raye-raye da wake-wake da maganganun batsa da ake yi a tiktok da finafinan Hausa. Manzon Allah ya ce farkon abin da za a fara ɗaukewa daga wannan al’ummar shi ne kunya da kuma amana:

“أول ما يرفع من هذه الأمة الحياء والأمانة.”

A rayuwar yanzu mutane masu amana sun yi matuƙar ƙaranci, a ɗakko mutum a saka shi a kan dukiya ko a ba shi aiki amma sai ya yi ha’inci. masu ayyukan hannu idan suka yi maka lissafi ka ba su kuɗi sai sun ƙara kudin, idan kuma kayayyaki suka yi ragowa su tafi da su, wannan duka cin amana ne.

Karanta Wannan  Najeriya ta tabbatar da kashe sojojinta shida a Borno

A halin yanzu idan ka kasance mutum mai gaskiya da amana ba za ka baɗa haɗin kai a yi cuta ba to za a kawar da kai. Wannan duka yana cikin alamun ƙarshen duniya. Allah ya ba mu ikon gamawa da duniya lafiya.” – Sheikh Dr. Isawa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *